An ja hankalin jama’ar Najeriya musamman na yankin arewa, da cewar su mayar da al’amurra ga Allah sannan su dage ga yin addu’o’i na samun zaman lafiya a yankin Arewa,domin halin da muke ciki yanzu ya biyo bayan abin da muka shuka ne.
Mai martaba Sarkin Birnin Gwari Alhaji Zubairu Jibirin Mai Gwari na Biyu ya yi wannan jan hankali, a yayin da yake gabatar da gajeruwar huɗuba kafin zuwan Liman a babban Masallacin Juma’a na Sarkin Musulmi Bello da ke garin Kaduna.
Mai martaban ya ƙara da cewar, yankin Birnin Gwari yanki ne da ya dade yana fama da marsalar rashin tsaro tun daga kan garkuwa da mutane har ya zuwa satar shanu sama da shekaru 20, amma cikin ikon Allah jama’ar gari suka tashi tsaye wajen maganin matsalar, sai dai abin takaici shine abubuwa sun ƙara lalacewa ne bayan zuwan mulki na siyasa.
Zubairu mai Gwari ya cigaba da cewar, a yau a Najeriya musamman yankin Arewacin Najeriya abubuwa sun dagule, dukkanin abubuwan baɗala da ba’a san dasu ba a baya, yanzu ana aikata su a yankin, Miyagun abubuwan kamar luwaɗi da Maɗigo sun zama ruwan dare, da wannan kaɗai Allah zai iya azabtar da mu.
Daga karshe Sarkin na Birnin Gwari ya shawarci jama’a da komawa ga Allah tare da yi wa kawunan su hisabi kafin zuwan kamun Allah.
Aika Labarin:
This content was originally published here.
VOTA PARA EVITAR LA DICTADURA
SALVA Al EDOMEX, UNIDOS SOMOS MAYORÍA
TENEMOS SOLO UNA OPORTUNIDAD
EL 4 DE JUNIO DEL 2023 VOTA PARA MANTENER
TU LIBERTAD, LA DEMOCRACIA Y EL RESPETO A LA CONSTITUCIÓN.
SI NO VOTAS PROBABLEMENTE TU VOTO NO VOLVERÁ A CONTAR
UBICA TU CASILLA AQUÍ
EL 2 DE JUNIO DEL 2024 VOTA PARA MANTENER
TU LIBERTAD, LA DEMOCRACIA Y EL RESPETO A LA CONSTITUCIÓN.
VOTA POR XÓCHITL









Comentarios